advanced Search

Wannan tambayar ta kunshi tambayoyi da yawa. Dangane da matsayi na musamman  da Imam Husaini (a.s) ya kebantu da shi, ya zo a ruwayoyi da hadisai na Musulunci.  Daga cikin tambayoyin shi ne suma sauran Ma'asumai Imama (a.s) suna da wadannan darajojin?

Tabbas ga duk mai yawan bincike a kafafen tarihi da hadisai zai ga abin da Imam Husain (a.s) ya rabauta da shi na jan hankali, darajoji da matsayi shi ya sa ba ma ganin akwai wasu sama da shi a matsayi da martaba.

  1. Imam Husaini (a.s) ya kebanta da kasantuwar Imamai daga tsatsonsa suke. An ruwaito daga Imam Muhammadul Bakir (a.s) yana cewa: "Allah Ya musanyawa Imam Husain saboda kisa da aka masa dukkan Imamai (a.s) daga tsatsonsa su ke.  Sannan Turbarsa magani ce. Kuma a kabarinsa ne ake amsar Addu'a nan take.[1] 
  2. Hadisi ya gabata da ke cewa Turbarsa (a.s), magani ce. To a nan ne zamu gane muhimmancinta musanyawa Imam Husain (a.s), ta hanyar maida turbarsa[2] Amma ya kamata musa shi bisa doron hukunci na Fikihu baya halasta amfani da ita fiye da kima, ma'ana kada girman Turbar Imam Husaini (a.s) da za’a yi amfani da ita ta wuce gwargwadan kwayar wake! [3].
  3. Amsa addua a kabarin Imam Hussain (a.s), wannan ma yana daga cikin karamomin da Imam Husain (a.s) ya banbanta da shi, wanda ba Imam Bakir kawai ya bayyana hakan ba, akwai wasu ruwayoyi ma daga Imam sadik (a.s) da kuma Imam Hadi (a.s) wanda ya ma taba tura wanda zai masa addua a farfajiyar Imam Husain (a.s), kamar yanda ya zo a ruwayar da abu hashim Ja’afari ya rawaito: “sanda Imam abu hasan al’hadi ya yi rashin lafiya sai ya ce ku tura wani zuwa ha’ir (wato hubbaren Imam Husain)[4] sai na fadawa Ali bn bilal hakan, sai ya ce: mai za ayi a can ha’ir din? Alhalin yana ha’ir din. Sai na zo wajen Imam al-askar na shiga inda yake sai ya ce min zauna, yayin da na so na mike. Yayin da na ga ya kebanta da ni, sai na gaya masa maganar Ali bn bilal, sai Imam ya ce: shin me ya sa baka fada masa cewa manzon Allah yana dawafi a ka’aba yana subbantar hajjarul aswad alhalin alfarmar Manzo (s.a.w) da ta muminai ta fi alfarmar dakin ka’aba amma duk da haka Allah ya umarce shi da ya tsaya a arfa, domin su ai gurare ne da Allah ya ke so a ambace shi a wurin. Saboda haka ni ina son a min addua gurin da Allah yake so, domin duk alkhairi yana wadannan gurare[5].
  • Sallah a hubbaren Imam Husain (a.s):

Sanannen abu ne a wajen malaman fikhu kamar yanda suka tabbatar a cikin risalolin su cewa matafiyi zai yi kasaru a sallah idan ya cika wasu sharuda da suka wajabta yin hakan. Amma duk da haka an toge wasu gurare da mai sallah kan iya zabi ko dai yayi kasaru ko ya cika daga cikinsu akwai hubbaren Imam Husain.[6]  akwai ruwayoyi da suke magana dangane da wannan fage da suke karfafa hukuncin sharia kan hakan, suke kuma nuna muhimmancin hubbaren da tsarkinshi[7]

Wannan ita ce dunkulalliyar tambaya na kashin farko. Amma bangaren tambaya ta biyu shin sauran Imamai ma’asumai suma suna da irin wadannan karamomi na Imam Husain?

Amsar wannan tambaya ita ce:  cewa, dukkan Imamai duk da kasancewarsu ma’asumai kuma da mukaminsu na wilaya takwiniyya (umarnin yi musu biyayya) sai dai ba zai yiwu ya zamana martabobinsu da mukamansu su zama daidai wadaida ba, a zance na ilimi ba abin da zai hana a tabbatar masu da matsayin wilaya -a mataki na tabbatarwa- indai har akwai shakka. Sai dai ba mu da wani dalili da zai tabbatar mana da wannan wajibcin. A wani zancen: ba abin da zai hana matsayi na isma -a kan kansa- na wani Imamin ya fi na wani saboda samun wasu mukamai da darajoji da suka kebanta da wannan Imamin. Sai dai ba wani dalili dake tabbatar da banbanci tsakanin su ya kan samu ne saboda wancan yanayi. Abin da hankali zai karba shi ne su sun daidaita a mukamin isma da wilaya ba wanda ya fi wani. Sai dai za a samu wasu dalilai na daban da kan sa Allah madaukaki ya ba Imam Husain wancan babban matsayi da kuma manyan karamomi.

Dangane da batun cewa wancan dalilin shi ke haifar da fifiko a tsakanin su duk kuwa da cewa dukkan su ma’asumai ne wanda za a yi wa wilaya Zamu iya nuni izuwa ga wasu abubuwa da ke tabbatar da wadancan batutuwan

  1. Kasancewar ma’asumai na massala dan adam wanda ya kai makura a kamala, sannan kuma ababen koyi mafiya daukaka ga dan adam kan tafarkin shiriya da nusantarwa, da wannan to ya zama wajibi ga kowanne Imami da ya dauki wasu matakai da kuma mafita wacce da su ne zai zamo abin koyi kuma jagora da za su zamar masa fitilar haskawa domin ya sanar da dan adam ta hanyar kyawun dabi’unsa, da kuma daukar matakai daidai da yanayin da yake rayuwa a cikinsa. Idan sulhu ne ya kama to sai su yi sulhu, idan kuma yanayi ya hukunta yaki sai su yi masa shiri da fuskar da ta fi kyau. Da wata ma’anar kuma, da gaskene cewa dukkan Imamai suna massala tajallin suffofin ubangiji ne mafiya cika, amma wasu dalilai ne da kuma yanayoyi na zamuna kebantattu ke sanya bayyanar wasu fuskoki na mutuntakar wannan Imami da kuma bayyanar su a aikace. Sai ya zamo kowanne Imami mai bayyanar da wani suna ne daga cikin sunayen ubangiji wanda ya dace da wannan yanayin ya kuma dace da wannan abin da ya faru. Ba shakka cewa zamanin da Imam Husain ya samu kan shi da kuma yanayoyin da ya rayu a cikinsu a ranar ashura sun bayyanar da abubuwa da yawa da kuma kamalar da take boye cikin mutumtakar Imam Husain (a.s) wadanda ba su bayyana ga sauran Imamai ba, ta yanda a wannan rana ta ashura (ranar da aka rayar da musulunci da kuma manya manyan martabobin manzon Allah, aka kuma ceto musulunci daga karkacewa da zamewa, da kuma bayyanar da muhimman abubuwa a cikin addinin musulunci) madaukakan darajoji da kuma madaukakan martabobi na Imam Husain (a.s) da sahabbansa sai suka bayyana. To wannan kamar yanda yake a dabi’ance wani nauyi ne da ya hau kan wuyansu, sannan kuma kowanne Imami yana da aikin da ya hau kansa wacce ta kebanta da shi, gaba dayansu sun hadu ne domin su zamo abin koyi da bada jagoranci da zai ke haskaka hanya da su. Bisa gaskiya, yanayi da sharuda na musamman su kan taka rawa wajen bayyana suffofin ubangiji da madaukakan darajoji. A nan ne zamu ga cewa lallai Imam Husain a ranar ashura ya bada wani kyakykyawan darasi, mafi kyan abin lura, da kuma mafiya kyawun matakai da suka sanya al’ummar musulmi kan iya alfahari domin su yi gasa da sauran al’umma albarkacin wannan babban mutum mai kawo gyara. Wannan ita ce gagarumar gwagwarmaya ta gyara da aka taba yi. Raya ashura daidai yake da raya ambaton ahlul bayt (a.s) gaba dayansu, sannan muhimmantar da karbala yana nufin muhimmantar da wadancan darussan da karbala ta samar da su ga al’umma. Manufa a nan ta raya bukukuwan karbala karfafawa ne domin kada a manta da wadancan dabi’u kyawawa, duk wanda ya raya ambaton Imam Husain (a.s) to kamar ya raya ambaton dukkanin ma’asumai ne gaba daya.
  2. Babu shakka Imam Husain ya yi shahada ne a ashura tare da sahaban sa managarta ta mafi munin hanya na kisa, kuma ya fuskanci mafi tsananin nau’i na jarrabawa da gwaji da kuma haduwa da manyan musifu wadanda ba wani wanda daga cikin masu gyara ya taba fuskantar irinsu, dukkan abin da ya samu annabawa da Imamai in ka auna kadan ne daga cikin abin da ya faru a ranar ashura da ya sanya sama da kanta ta koka[8]. To wannan babbar wakiar dole a raya ta domin ta bada darasin da ya dace gwagwardon matsayin mai wannan yanayin. A ta nan zamu iya fahimtar cewa ashe Imamai (a.s) suna karfafa wannan lamari na ambaton Allah a ko wanne lokaci a kuma ko wanne zamani[9]

 

 


[1] Almajlisi muhammad bakir, biharul anwar j 44, sh 221 mu’assatul wafa bugu na daya (1404h).

[2] Kamar yanda ya gabata a na daya.

[3] Taudihul masa’il (al’muhusha na Imam khomein) j 2 sh 598, mas’ala ta 2628.

[4] Biharul anwar (zancen sa (a.s) na “ku tura wani zuwa ha’ir (yana nufin hubbaren Imam husain (a.s) ya min addua ya kuma roki allah ya warkar dani) j 9, sh 112.  

[5] Biharul anwar j98, sh 112.

[6] Taudihul masa’il (almuh’sha na Imam khomein) j1 sh 728 mas’ala ta 1356, Almailani, sayyid muhammad hadi, muhadarat fi fikhul Imamiyya j 1, sh 31.  

[7] Alhurr al’amily alshaikh muhammad bn hasan, wasa’ilush shia j8, sh531, almajlisy muhammad bakir biharul anwar, j86, sh 88, shaikh mufid, almizaar 140.

[8] A nan yana nuni ne da cewa “ni ne dan wanda mala’ikun sama sukai kuka da rashinsa, nine wanda aljanu sukai kururuwa da rashin sa a bayan kaa, da kuma tsuntsaye a sama......” almajlisy, biharul anwar muassasatul wafa’i, lebnon. 1404h.  

[9]  Saboda neman karin bayani a na iya duba littafin: tarkhan, kasim narkashy irfany, falsafy wa kalamy.

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa