Please Wait
Dubawa
5457
5457
Ranar Isar da Sako:
2017/01/07
Takaitacciyar Tambaya
Me ya sa a msulunci awkai wurare da aka bada damar a doki yaro karami?
SWALI
Me ya sa muslunci ya halasta dukan yaro karami a wasu wurare?
Amsa a Dunkule
Addinin muslunci na ganin tsarin tausayi da jin kai da tausasawa ita ce hanyar da ta fi tasiri fiye da ragowar hanyoyi, duk da cewa a wasu wurare ya zama tilas idan yaro aikata wani nau'in kuskure a ladabtar da shi ta hanyar dukansa a sakamakon aikin da ya aikata, saboda idan ya zamanto cikin munana ayyuka misalin yin sata ko lalata dukiyar wasu ba a dauki matakin da ya dace kan shi ba, to munana ayyuka zasu wayi gari al'ada gare shi, zai saba da aikata su, saboda haka ana iya amfani da wata hanya domin ladabatar da shi ba tare da an doke shi ba, amma fa dole hanyar da za abi ta zamanto ta dace da hankali kamar misalin dena yi masa magana da yanke dangantaka da shi, a dena zuwa da shi yawon shan iska , a hana shi fita wasa da hana shi yin abubuwa da yake da tsananin alaka da su, misalin irin wannan mataki na ladabtarwa, matukar an gudanar da shi ta yadda ya dace zai matukar tasiri da fa'ida cikin tarbiyyar yaro.
Wani mutum cikin hallarar imam musa kazim ibn jafar (a.s) ya kawo kukan dansa sai Imam Musa (a.s) ya ce da shi: kada ka doki danka, ka yanke alaka da shi domin ladabtar da shi, sai dai cewa ka yi taka tsatsan ka da yanke alakar ta dauki lokaci mai tsayi.[1]
Bisa lura da abin da bayaninsa ya gabata bisa asasin ba'arin wasu riwayoyi an baiwa waliyyan yaro da masu yi masa tarbiyya izini a lokacin larura suna iya yin duka don tarbiyantar da yaro. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: yayin da yara suka kai shekaru bakwai ku umarce su da yin salla lokacin da suka kai shekaru tara idan suka bar yin salla ku doke su, yayin da suka kai shekaru goma ku raba musu wajen kwanciya.[2] Haka ma imam Ali (as) yana cewa: da wannan hanya da kuka ladabtar da `ya`yanku to ku ladabtar da marayu, a duk inda su ka yi wani aiki da ya sanya ku dukansu to suma marayu idan suka yi irin wannan ku doke su.[3]
A addinin musalunci sanannen abu ne cewa ladabtarwa ba ta nufin huce haushi ko daukar fansa daga mai laifi, kadai dai ladabtarwa na kasancewa domin amintar da hakkokin mutane da samar da aminci cikin zamantakewa da kiyayewa daga fadawa rashin tsari, wannan shi ne hadafin tarbiyya, sabboda haka ne ma muslunci ke kallon tarbiyar gangar jiki da wadda bata gangar jiki a matsayin hanyoyin[4] tarbiyya da kuma aiki da su cikin wuraren da yin aiki da su ke bada fa'ida.
Ya dace a bada lura: duk da kasantuwar ladabtarwar jiki na tsawatarwa yana hana yaro aikata laifi sannan an dauke shi a matsayin matakin karshe wanda zai iya zama daya daga cikin hanyoyin ladabi, sai dai cewa yana da matukar hatsari galibi ma bai dacewa , bisa hakika ana ganin matakin duka a matsayin mataki na karshe, saboda na iya yiwuwa yaro saboda tsoron ladabtar da shi a zahirance ya dena abin da yake aikatawa a lokacin da yake gaban iyayensa ko masu tarbiyantar da shi, sai dai cewa hakan ba ya nufin ya yi watsi[5] da mummunar ala'adarsa. Kai hatta hakan zai iya kawo cutarwa kamar haka:
1-yaro zai saba da tilashi, ba tare da tamtama ba, dole a sallama a wannan tunani na nuna karfi da duka yaro ne zai yi nasara ba masu dukansa ba.
2- yaro zai dinga jin yana tsanar kiyayyar mai dukan sa sannan yaron zai samu kwarin juciya kan yi msa tawaye.
3- yaro zai wayi gari da ruhin yawan jin tsoro da rauni kuma daidaitar ruhinsa zata sakwarkwace.
Bisa la'akari da mummunan gurbin jiki, Imam Sadik (a.s) yana cewa: ba a yi wa yaro haddi, sai dai cewa ana ladabtar da shi ta hanyar yi nasa gyara da nusar da shi.[6]
Ance; ya kamata idan za a doki yaro to ayi ta yanayin da ba zai sanya ka biyan diyya ba, idan dukan ya kai ga halaka yaron tabbas za a yi wa wanda ya doke shi kisasi ko kuma ya biya diyya, idan ya kasnce sakamkon dukan daya daga cikin gabban yaro ya nakastu ya zama wajibi ya bada diyya.[7] Saboda haka wanda aka ba shi izinin yin duka cikin tarbiyar yaro ya kamata ya yi taka tsantsan kada ya ketare gwargwadon iyakar da aka yi masa izini kada ya tsananta duka ta yadda za tai kai shi da tsayar da kisasi a kansa ko biyan diyya.

[1] Uddatu da'I wa najahu sa'I ibn fahad hulli jamalul dini ahmad ibn Muhammad sh 89 bugun darul kutub arabi
[2] Ibn hayyun magaribi nu'uman ibn mohd cikin da'a'imul islam wa zikrul halal wal haram wal kadaya ahkam juz 1 sh 194 mu'assasatu ahlul baiti kum bugu na biyu shekara ta 1385. Ibn abi jamuru ihsa'I mmohd ibn ali cikin awali li'ali aziziyajuz 1 sh 252-253 kum darul sayyid shuhada lil nashar bugu na farko shekara 1405
[3] Kafi j 6 shafi na 47.
[4] Islam wa ta'alim tarbiyya sh 253-255 kum bustanu kitab bugu na uku shekara 1387
[5] Farhadiyan rida anceh walidaini wa murabbiyan bayad bedanad sh 66 kum mu'assasatubustanu kitab bugu na 19shekara 1391shamsiyya
[6] 454juz 2 sh Da'a'imul islam wa zikrul halal wal haram wal kadaya wal ahkam
[7] Sayit diyyeh tanbihi farzand su'al 12643
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga